Advertisement

Yan bindiga sun far ma gidan yari, wasu da dama sun kubuta

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kula da lamuran gidan yari, Rabiu Shuaibu ya bayyana, an kashe wani jami'in hukumar sanadiyar arangamar da ya faru tsakanin yan bindiga da jami'an tsaro.
Advertisement

Lamarin ya faru a daren ranar lahadi a gidan yarin dake nan unguwar Tunga.

Advertisement

Wannan  yana daya daga cikin ire-iren harin kubutar da wadanda aka tsare a gidan yari da zai faru kwana-kwanan nan.

Ban jami'in hukumar, yan bindigar sun halaka wani mai babur wanda ke safarar ma'aikacin gidan yari.

Sai dai ba'a san adadin wadanda suka yi nasarar kubuta daga gidan kaso amma an kama wasu daga ciki su bakwai.

Rabiu Shuaibu ya kara da cewa hukumar zata yi iya bakin kokarin ta wajen kama wadanda suka gudu daga gidan kason.

Advertisement

Yayi kira ga sauran jama'a jihar da ma kasar da su taimakawa hukumar wajenn kama wadanda suka kubuta.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement