gabar da ya tsakanin jigogin masana'antar Kannywood har yanzu yaki lafawa inda mabiyan su sun cigaba da yi ma juna kalaman batanci a shafukan sada zumunta.
Ganin illar da yin hakan zai jawo ma mabiyan su musamman kananan jarumai, mawakin ya shawarci jaruman da su kawo karshen gabar da yaki cinyewa.
Ga yadda ya rubuta a shafin ta na Instagram:
"Ali nuhu naga alama kuna wasa da nauyin da ALLAH ya dora muku na jama ar dake karkashinku sannan kuna kokarin raunana imaninku domin kuwa alamomi suna nuni da baku dogara da ALLAH ba duba da tsoran da kuke nunawa junanku sannan duk lokacin da za kuyi rigimar me yasa bakwa barinta a junanku sai kun nemo ma biyanku kun jefasu a bala i sannan in zaku shirya bakwa nemansu hakan yana nunu da sankai da rashin adalci da rashin imani, kawai ku mafitarku kuke dubawa bakwa duba ta wasu? Wanda suke shiga rigimarku su sai da rai suna rasa abinci a cikin masana antar kannywood dalilin rigimar ku wanda da baku sasu a ciki ba za suyi mu amala da kowa kuma su nemi halak dinsu amma in kuna rigima wannan ba zaiyi aiki da wannan ba wannan bazai gaisa da wannan dan kawai bakwa shiri kuna haifar da gaba da tashin hankali.
da rashin zaman lafiya shine soyayyar da kukewa kannywood din? Ko shine taimakon nakasan da kuke ikirarin kunayi?ku cire girman kai ku cire rawunan da kuka
dorawa kawunan ku na san girma wane ne sarki wane ne yarima dukanin ku babu wanda aka nadawa wata sarauta duka ku kuka sawa kanku in kuma da wanda aka nadawa wani rawani ya fito ya fadawa duniya wuri da kuma lokacin da akayi nadin babu Sarki sai ALLAH haka kuma babu abin dogaro sai shi daga ALLAH sai ANNABI sune masu girma kowa a kasa yake ba wanda yafi wani sai wanda yafi tsoran ALLAH amma kun kasa gane hakan
in kunga dama ku gyara a zauna lfy idan kuma baza ku gyara ba bakin ciki zaisa kui tayin baya kun cutar da kanku kuma kun cutar da wasu karshen mugunta kenan ra ayi na ba irin na kowa bane kuma banyi dan yabo ko kuma neman wani abu a gun daya daga cikin kuba dama bantayi ba kuma InshaAllah bazanyi ba dan ALLAH nayi kuma inaso na kasa su daina cutuwa bana raina yaro kuma bana raina babba ina son kowa da karuwa ne ba iya kaina ba duk wanda yaji haushi bazan bashi hakuri ba gaskiya ce sai na fada komai dacin daza tayiwa wasu a karshe ina kira ga duk wanda yasan yana tsoran rasa abinci gun wani kada yayi reposting ni dai babu mai bani sai ALLAH Alhamdulillah".
Duk da cewa jaruman sun sulhunta tsakaninsu a kwanan baya, rikicin nasu bai lafa ba.