Majalisar wakilan tarayya ta gargadi babban bankin Nijeriya ta CBN kan illolin gurbatattun naira da suka mamaye kasar.
Dan majalisa Honourable Adekoya Abdel-Majid mai wakiltar yankin Ijebu-North/Ijebu-East na jihar Ogun karkashin inuwar jam'iyar PDP ya shigar da kudirin a zaman majalisa da aka gudanar ranar laraba 18 ga watan Yuli.
A labarin da jaridar The nation ta fitar dan majalisar yayi la'akari da gurbatattun naira dake neman mamaye kasar musamman naira 100.
Yace kananan hallitu masu haifar da cuta sukan samu wajen cigaba da rayuwa a wurare masu datti kuma yawan su ya kan haifar da illa ga lafiya dan adam.
Dan majalisar ya umarci babban bankin da ta yi gaggawa wajen fitar da gurbatattun nairori daga bankuna dake fadin kasar kuma ta sauya shi da sabbi.
Majalisar ta umarci kwamiti kan harkokin bankin da kudi da tayi bincike kan kasuwar siyar da sabbin kudade a sassa daban-daban na fadin kasar.