ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna yayi amai ya lashe, yace har yanzu shi dan APC ne sabanin ikirarin da yayi kwanan baya

Gwamnan ya yi amai ya lashe ne bayan tattaunawar sulhu da suka yi da tsohon gwanan jihar Benue karkashin jagorancin Shugaban jamiyyar Adams Oshiomhole a ranar Alhamis.

wannan bayanin ya biyo bayan ikirarin da yayi ranar litinin 16 ga watan Yuli na cewa ya fice daga jam'iya mai mulki.

A yayin da ya dauki wannan matakin ya bayyana cewa bai zabi jam'iyar da zai koma ba.

Sai dai uwar jamiyyar APC ta maida martini cikin gaggawa inda ta ce basu raba-gari da gwamnan ba, sannan ta gayyace shi da kuma tsohon gwamnan jihar Benue Sanata George Akume zuwa sakatariyar jam'iyyar domin su yi tattaunawar sulhu.

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya yi amai ya lashe ne bayan tattaunawar sulhu da suka yi da tsohon gwanan jihar Benue karkashin jagorancin Shugaban jamiyyar Adams Oshiomhole a ranar Alhamis.

A labarin da BBC ta fitar gwamnan yana mai cewa:

"Na zo ofishin jami'yyar APC a matsayi nan a dan jam'iyyar APC, kuma har yanzu ina rike da tutar jam'iyyar. Na ce mun yi hannun riga da jamiyyar APC amma uwar jam'iyyar ta yi min gyra,"

"Mun raba-gari da Jamiyyar APC ta jihar Benue kuma shi yasa na ga ya dace na fice sai dai shugabannin uwar jam'iyyar sun ce matakin da uwar jam'iyyar ta dauka ya fi duk wani mataki da wani ko wasu za su dauka a cikin jiha kuma a gani na wannan ya yi dai - dai."

Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jam'iyar APC ke fuskantar rikici a fadin kasar wanda ya kai ga samun bagarori a cikin.

ADVERTISEMENT

Wani sabon akida ya bullo a jam'iyar wanda take kiran kanta da rAPC kuma Buba Galadima ke jagorantar su tare.

rAPC tayi ikirarin tawaye daga uwar jam'iyar tare da kafa nashi tsarin shugabanci.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT