A yayin da masoya da magoya bayan zarcewar shugaba Muhammadu Buhari ke hada kai wajen hada kudin siya ma shugaban takardar neman takara ta APC, wata kungiyar ta musamman ta daukin nauyin samad da takardar.
Kungiyar mai suna Nigerian Consolidation Ambassadors Network ta mika kudin (N45M) na fom din takarar shugaban a hedkwatar jam'iyar APC dake nan Abuja.
Lamarin ta wakana ranar laraba 5 ga watan Satumba a gaban shugaban jam'iyar Adam Oshiomole tare da sauran jagororin APC.
Jagoran kungiyar Sanusi Musa kaddamar da takardar takarar bayan ya mika kudin ga uwar jam'iyar.
Sanusi ya shaida cewa ya'yan kungiyar tunda daga karkara da kananan hukumomi na jihohin kasa suka hada kudin siyan takardar domin nuna gamsuwar su ga shugabancin shugaba Buhari.
Kungiyar tace ta amince da mulkin shugaban wanda ya sanar da anniyar sa na zarcewa kan karagar mulki.
Lamarin dai ya faru bayan kwanan daya da jam'iyar APC ta fitar da jadawalin kudin siyan takardar tsayawa takara na kon wani kujerar siyasa.
Kamar yadda jadawalin ta bayyana adadin kudin siyan takardar takarar shugaban naira miliyan 45 (N45M).
Fom din takarar gwamna ta tsaya a kan N22.5M yayin da na majalisar dattawa yake N7M.
Haka zalika takardar takarar majalisar wakilan taraya ta tsaya a kan N3.8M kana na majalisar jiha ta tsaya a N850,000.