Advertisement

Mata biyu yan kunar bakin wake sun rasu sakamakon tashin bam da suka dauka

Kakakin, Edet Okon, ya tabbatar da faruwar hakan a cikin wata takarda da ya fitar ranar alhamis 21 ga wata a garin Maiduguri.
Advertisement

Wasu yan kunar bakin wake biyu sun rasu yayin da suke shirin tayar da bam a garin Maiduguri.

Advertisement

Kamar yadda kakakin rundunar yan sanda na jihar Borno ya sanar, yan fashin mata biyu ne kuma basu yi sa'ar cinma manufar da suke nema.

Kakakin, Edet Okon, ya tabbatar da faruwar hakan a cikin wata takarda da ya fitar ranar alhamis 21 ga wata a garin Maiduguri.

Jami'in yace mai dauke da na'urar na farko ta gamu da ajalin ta sakamakon harbin da sojoji suka yi mata yayin da take yunkurin cusa cikin jama'a a kasuwar mamy na barikin sojoji. Sojojin sunyi hakan ne bayan sun zargi ta da daukar bam a jiki.

Ya kara da cewa na biyun ta rasu ne bayan ta tayar da na'ura bam a cikin keke mai kafa uku kuma mai tukin ya tsira daga faruwar hakan.

Advertisement

Daga karshe yayi kira ga sauran al'ummar jihar da su cigaba da kula da abubuwa dake faruwa a tsakanin su kuma suyi gaggawa wajen sanar ma jami'an tsaro duk wani abu da suke shakku a kai.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement