Advertisement

Maryam Sanda ta samu hukunci damar yin beli kan laifin kashe mijinta da ake tuhumar ta

Mai sharia Yusuf Halilu ya zantar da hukuncin a zaman kotu da aka yi safiyar ranar laraba a birnin tarayya
Advertisement

Bisa rahoton da TheCable tafitar mai sharia HaliluYusuf ya zantar da hukuncin yin beli a zaman da aka yi yau laraba 7 ga watan Maris 2018 bisa bayanin da ta fitar mai cewa tana dauke da juna biyu.

Advertisement

Alkalin ya nemi kotu da ta bayar da damar beli ga Maryam bisa cikin da take dauke dashi wanda ya kai na tsawon wata uku.

Kasancewa an daure Maryam a gidan kaso kuma daga nan take ziyartar dakin sauraron kara,  alkalin ya nemi kotu da ta ba maryam damar cigaba da halartar kotu kan karar da aka shigar kanta daga gida domin kula da juna biyun da take dauke dashi.

Ana tuhumar ta kan zargin kashe mijinta Bilyaminu Bello dan tsohon shugaban jam'iyar PDPBello Halliru a gidan su dake nan garin Abuja.

Advertisement

Wannan lamarin ya tada kura a kasar inda jama'a da dama sunyi tsokaci game da faruwar hakan.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement