ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Daga baya Atiku ya koma tsohon gidan sa ta jam'iyar PDP

Yana mai cewa "na dawo gida" domin babban dalilin da ya sanya na bar jam'iyar PDP an warware ta

Ya sanar da haka a kafar safar sada zumunta ta facebook kai tsaye ranar lahadi 3 ga watan Disamba.

Yana mai cewa "na dawo gida" domin babban dalilin da ya sanya na bar jam'iyar PDP an warware ta.

Shi dai Atiku Abubakaryayi murabus daga jam'iyar APC cikin makon da ya gabata inda yake yiwa jam'iyar zargin cewa bata cinma burin yan Nijeriya ba kana  bata kwatanta hakikanin tsarin dimokradiya.

Karanta Tsokacin gwamna yayi game da ficewar Atiku daga jam'iyar APC >>Babu Mai farin jinin shugaba Buhari

ADVERTISEMENT

Ficewar shi daga Jam'iyar APC bata razanar da wasu da dama ba domin ana ganin cewa zai sauya zuwa jam'iyar PDP domin kaddamar da kuddirin sa na zama shugaban kasar Nijeriya a 2019.

Hirar sa da Dele Momodu, mai wallafa mujallar Boss magazine a cikin hutun karshen mako, Atiku ya sanar cewa Shugaba Buhari bai da farin jini kamar yadda yake dashi a da kana ya kara da cewa zai kada shugaban a zaben 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT