Babu wanda yake da farin jinin shugaba Buhari - Tsokacin da gwamna yayi game da ficewar Atiku daga Jam'iyar APC
Yayin da yake ganawa da manema labarai nan fada shugaban kasa dake villa ranar juma'a, gwamna Nasir El-rufai yace fitar da Atiku yayi daga jam'iyar APC baza taka wani rawan gani a idon sa domin sauran jiga-jigan jam'iyar na nan daramdamdam. Gwamnan ya kara sda cewa babu wanda ke da kwatankwacin farin jinin shugaba Buhari kuma babu wanda zai kada shi a zabe.
A kwanan baya gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yace Buhari ne mafi cancanta a zaben 2019.
Ana sa ran cewa shugaba Buhari zai bayyana aniyar sa na fitowa a zaben 2019 nan ba da dadewa ba.
Karanta labarin:Tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana anniyar sa na zaben 2019 (Ga bidiyo nan kasa)
Wata kila tsohon mataimakin shugaban kasa ya sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP inda ya samu damar fitowa takara a zaben 2011 duk da cewa bai bayyana aniyar sa na zuwa wata sabon jam'iya.