ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Bayan ziyarar da yakai yankin kudancin kasa, shugaba Buhari ya dawo gida da abun farin ciki

Ziyarar dai shine na farko da shugaban ya kai yankin tunda ya zama shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Abuja bayan ziyarar kwana biyu da ya kai jihohin yankin kudancin kasar.

Wannan shine karo na farko da shugaban ya kai yankin tunda ya hausa kujerar mulkin kasa.

Ziyarar wanda ya kaddamar ranar 14 ga watan nuwamba inda ya fara zuwa jihar Ebonyi. a jawabin sa yayin da yake kaddamar da wasu ayyuka a jihar shugaban ya bada kudirin gwamnatin sa na gabatar da ayyukan cigaba a yankin.

Bayan ayyukan  cigaba da shugaban ya kaddamar jihar Anambra da Ebonyi, ya samu sarautu daga sarakunan gargajiya na yankin inda aka nada shi da sarautar Enyioma 1 of Ebonyi (wato Abokin amana na jihar Ebonyi) da Ochioha Ndi Igbo 1 (jagoran yan kabilar ibo).

ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari yace zuwan sa yankin ayyah ce mai nuna cewa yana alfahari da al'adu iri-iri dake fadin kasar.

Daga karke shugaban ya nuna farin cikin sa dangane da sarautan da aka nada mai inda yayi ma sarakuna godiya da karramawa da suka yi mashi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT