ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugabanci ta tabbatar da sakin ƴan matan Chibok 82 da ake sace

Buhari ya gamsu da samun nasara wurin sulhu da ya kai ga sakin wasu ƴan mata.

___6644971___https:______static.pulse.com.gh___webservice___escenic___binary___6644971___2017___5___8___17___Chibok-girls

Shugabanci a ranar asabar, ta tabbatar da sakin wasu ƴan matan chibok 82 bayan shekara uku a kame.

Malam Garba Shehu, Babban mataimakin Shugaba na musamman a kan harkokin kafofin watsa labarai da bayanai cikin jama'a, ya tabbatar da sakin ƴan matan a wani sanarwa da ya sa a kafofin watsa labarai a ranar Asabar a Abuja.

Kakakin Shugaba ya ce Shugaban ƙasa ya gamsu da samun nasara wurin sulhu da ya kai ga sakin wasu ƴan matan.

Ya sanar da cewa Shugaba ya kuma yaba al'umma na hukumomin yan tsaro saboda himman su a tabbatar da cewa an sake ƴan matan.

ADVERTISEMENT

A cewar shi, Shugaba zai gan ƴan matan da aka ceci a Abuja a ranar Lahadi.

Shehu kuma ya tabbatar cewa waɗanda suka kama ƴan matan sun sake su a musayar wasu da gwamnatin tarayya ke zargi da cewa yan Boko Haram ne.

Sanarwar ta ce : "Shugaba Buhari na farin cikin sanarwa cewa sulhu da aka yi game da sakin sauran ƴan matan chibok ya sami nasara yau bayan watanni na haƙuri da tattaunawa. Hukumar tsaron mu sun amshi ƴan matan na da aka sace musayar wasu da gwamnati ke zargin yan boko Haram ne."

“Ƴan matan za su Iso Abuja gobe, Shugaba zai karɓe su. Shugaba ya nuna matuƙar Godiya ga hukumar tsaro, Sojoji, Gwamnatin Switzerland, Red cross, ƙungiyoyin ƴan ƙasa  tare da na ƙasa da ƙasa masu zaman kansu saboda samun nasarar wannan aikin.”

“Za a tuna lokacin da aka saki ƴan mata guda 21, a Oktoba shekara ta 2016, Shugaba ya bada umurni ga hukumar tsaro da cewa su cigaba da aiki har sai an saki duk ƴan matan Chbok da aka sace a mayar da su ga iyalan su.”

ADVERTISEMENT

“Shugaba ya na samun cikkaken rahotanni daga Direkta-Janar na tsangaya na harkokin Jihar a kowane mataki na aikin.”

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT