Advertisement

Ɗiyar shugaban ƙasa ta nuna facin ran ta game da karancin kayan aiki a asibitin Villa

Zahra Buhari tace masu jinya ke siya magunguna, sirinjin allura har ma da safar hannu da kudin su
Advertisement

Ɗiyar shugaban ƙasa Zahra Buhari ta nuna facin ran ta game da yadda allamura ke tafiya a asibitin dake fadar shugaban ƙasa.

Advertisement

Ta tabbatar da rahoton da aka yi a baya na cewa asibitin bata da cikakken kayan aikin da ya kamata.

Zahra ta nuna fushin ta a shafin ta na instagram ranar juma’a 29 ga watan satumba.

Tana neman amsa akan yadda aka kashe naira bilyan 3 daga cikin kasafin kudi da aka ware ma asibitin.

Zahra Buhari tace masu jinya ke siya magunguna, sirinjin allura har ma da safar hannu da kudin su.

Advertisement

A baya dai kakakin shugaban ƙasa Femi Adeshina yace bai san ko shugaban yana zuwa asibitin Villa domin ganin liƙita.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement