Advertisement
Buhari ya rattaba hannu ga dokar bada fifiko ga yan kasa fiye da yan kasar waje wajen bayar da kwangilar aiki.
Shugaban ya sa hannu ga wannan dokar jiya litinin 5 ga watan janairu a fadar sa dake nan Abuja.
Advertisement
"A cikin wannan doka ta shugaban kasa, Shugaban ya ba da umarni ga hukumomi da ma'aikatun gwamnati su rika bayar da fifiko ga kamfanonin cikin gida wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan tsaron kasa". kamar yadda fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter.
Advertisement
Shugaban yace an dauki wannan matakin ne domin samad da aikin yi ga yan kasa.
Shugaban ya haramtawa ma'aikatar cikin gida bayar da bisa ga 'yan kasashen wajen da za su shigo Najeriya domin gudanar da dukkan ayyukan da akwai wadanda ka iya yin su a kasar.
Sai dai shugaban yace dai, a inda ba' a samu yan kasa kwararu za' a iya bayar da kwangilar ga kamfanonin kasar waje.
Advertisement
Subscribe
Sportal WhatsApp
Latest Videos
Nigeria hausa
Gobara tayi sanad in mutuwar mutum 35
11.09.2018
Advertisement
Videos
Advertisement
Advertisement
More from Pulse Nigeria
Advertisement