Advertisement

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya soma fitowa a wasan kwaikwayo (Ga bidiyon)

Obasanjo ya haska cikin wani sabon shirin da Samuel Ajibola ke jagoranta
Advertisement

Shirin “Dele Issues” wanda Samuel Ajibola wanda aka fi sani da ‘SPiff’ ke jagoranta zai samu sabon jarumi a sabon shiri ta musamman wanda aka yi wa laƙani da “Dele for President”.

Advertisement

Shirin jerin wasan barkwanci ne kuma a sabon shirin da za’a fitar nan bada jimawa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya haska a ciki.

A cikin sumun-tabin bidiyo wanda aka sako Obasanjo yana goyon bayan jagoran shirin 'Dele' da ya fito takarar shugaban ƙasa.

za'a sako sabon shirin wanda tsohon shugaban kasa ya fito a ciki ranar asabar 14 ga watan octoba 2017.

Wannan shine fitowar shi na farko a cikin shirin wasan kwaikwayo kuma ya nuna basirar sa na yin wasan kwaikwayo a ciki.

Advertisement

Sauran jaruman masana’antar shirya fina-finai sai su zage damtse domin tsohon shugaban ƙasa ya fara fasowa a dandalin.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement