Ranar 8 ga watan maris na ko wace shekara majalisar dinkin duniya ta ware ta a matsayin ranar mata domin bikin nuna cigaban da mata suka kawo a duniya.
Bisa wannan dalilin muka kawo maku wasu matan arewacin Nijeriya fara kafa tarihi ta hanyar zamowa mata na farko da suka rike wani mukami. Ga su kamar haka:
1. Naja’atu Bala Mohammad
Naja’atu Bala Mohammad ce mace ta farko da ta zama shugabar kungiyar daliban jami’a a Najeriya. An haife ta a garin Kano a shekarar 1966. Ta zama shugabar dalibai lokacin tana karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
2. Amina Muhammed
Amina Muhammed ce mace ta farko 'yar Najeriya da ta zama mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya. 'Yar asalin jihar Gombe ce kuma an haife ta a shekarar 1961. Ta samu wannan mukami a watan Fabrairun 2017.
3. Justice Maryam Aloma Mukhtar
Justice Maryam Aloma Mukhtar ita ce Mace ta farko da ta zama babbar mai shari’a a Najeriya. An haife ta a 1944 kuma 'yar asalin jihar Kano ce. Ta samu wannan mukami a shekarar 2012.
4. Farfesa Fatima Batoul Mukhtar
Farfesa Fatima Batoul Mukhtar ita ce Mace ta farko da ta zama shugabar jami’a a arewacin Najeriya. An haife ta a 1963, 'yar asalin jihar Kano ce. Ta zama shugabar Jami'ar Tarayya da Dutse a 2016.
5. Justice Zainab Bulkachuwa
Justice Zainab Bulkachuwa ce Mace ta farko da ta zama babbar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya. An haife ta a 1950 kuma 'yar asalin jihar Gombe ce. Ta samu wannan mukami a shekarar a 2014.
Banda su, ku bayyana sauran matan arewa da su suka taka rawar gani bisa gudunmawar da suke bada wa wajen raya al'ummar mu.