Advertisement

Ba sauki ga duk wani ma'aikacin hukumar da aka kama da laifin zamba

Magu ya sanar da haka a wani hulɗa da yayi da mawallafa a Abuja ranar laraba
Advertisement

Mukaddashin Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahim Magu ya bayyanar cewa akwai wasu daga cikin jami’an hukumar wanda karar su na gaban kotu.

Advertisement

Magu ya sanar da haka a wani hulɗa da yayi da mawallafa a garin Abuja ranar laraba.

Duk da cewa bai sanar iyakar ma’aikatan da ake zargi da aikata laifi, shugaban ya jaddada cewa ba zai sassauta ma duk wani ma’aikacin hukumar da aka kama da aikata laifin cin hanci.

Shugaban ya ayyana cewa hukumar ta sallami wasu jami’an ta kasancewa sun samu matsala da takardar shaidar su na makaranta. Ya kara da cewa an kai karar wasu gaban kotu.

Magu ya sanar cewa yakin ganin an kawar da cin hanci da rashawa a ƙasar ya karfafa kuma yana neman taimakon jama’a wajen ganin cewa sun cinma burin su musamman kafofin watsa labarai.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement