Dan wasa mai tauraro zai kasance tare da Barcelona a cewar abokin hamayyar sa na ƙungiyar Barcelona Gerard Pique a shafin sa na twitter.
Mai tsaron bayan ƙasar Spain ya tabbatar cewa Neymar yana nan daram-dam-dam a barcelona inda ya dora hoton dan wasan tare da rubata “babu inda za shi”.
Wannan sakon ya fito sa’o’i kadan bayan dan wasan ya nuna halin shi ne mai ƙwazo inda ya saka ƙwallo biyu a raga a wasan ƙawance da ƙungiyar Barcelona suka buga da Juventus wanda Barcelona ta doke Juventus 2-1 ranar asabar a garin New jersey.
Akwai jita-jita dake yaduwa na cewa dan wasan zai koma PSG don ƙungiyar ta shirya biyan makudan kudi don ganin shi a ƙasar Faransa.
Mai horon ƙungiyar Barcelona Ernesto Valverde yayi watsi da jita-jitan inda yace dan wasan zai cigaba da buga wa ƙungiya don tawagar na son ya zauna tare da su har shekaru da dama.
Neymar tare da sauran yan Barcelona na shirin bugawa da Manchester United a wasan ƙawance ranar laraba 26 ga watan Yuli a birnin Washington.