Advertisement

Minista yayi juyi kamar mazari cikin kayan gargajiya wanda aka yi da fatar damisa (bidiyo)

A cikin bidiyon zaku gan yadda Ministan ke taka rawa tare da rike adda a hannun sa yayinda ake bikin gargajiya
Advertisement

Nijeriya ta samu kari daga cikin manyan yan siyasa masu tika rawa inda shima ministan mai Ibe Kachikwu ya fitar da basirar sa a wata bikin gargajiya da aka gudanar a jihar Delta.

Advertisement

Cikin bidiyon zaku gan inda ministan ke juyi kamar mazari tare da rike adda a hannu cikin kayan gargajiya wanda aka yi da fata damisa.

Bikin wanda aka yi yankin  Onicha Ugbo na jihar ranar asabar 30 ga watan Satumba domin nuna farin cikin fitowar sabon doya (wato new yam festival) ministan yayi rawa a titi tare da sauran al’ummar garin har ma wani na taimakon shi da rikon bindin kayan da ya sanya.

Ministan dan asalin yankin Onicha Ugbo ne kuma yana riƙe da babban mukami a garin.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement