Advertisement

Mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan tsarin kula da abubuwa dake gudana a yanar gizo

kakakin shugaban kasa
kakakin shugaban kasa
Shehu yace umurnin babu wani kuskure game da umurnin indai zai taimaka wajen magance kalaman tunzura
Advertisement

Babban mataimakin shugaban kasa akan harka labarai Garba Shehu yace umurnin da uban gidansa ya bada na lura da abubuwa dake gudana a yanar gizo bai yi tsauri ba.

Advertisement

Bisa ga labarin da Dailypost ta fitar, Shehu yace umurnin bai yi tsanani ba indai zai taimaka wajen magance kalaman tunzara.

Kakakin shugaban kasa ya fadi haka yayin da yake amsa tambayoyi a wani shiri da gidan talibijin na Channels televisions suka gabatar ma take “politics today”.

Shehu ya bayana cewa yawancin ta’addanci dake yaduwa a kasar da ma duniya baki ya kan farawa daga yanar gizo.

Ya kara da cewa dole a tantance tsakanin kalmomi masu ma’ana da kalaman tunzura.

Advertisement

Game da batun mai ba shugaban kasa shawara akan alamuran yan majalisa Sen. Ita Enang yace umurnin bai sabawa dokar ‘yancin furtar da magana da makamancin haka.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement