An haifi jarumin mai tauraro wanda aka yi ma lakabin sarkin Kannywood a garin Maiduguri ranar 15 ga watan Maris na shekara 1974.
Yayi karatun kuruciyar sa a jihar Kano kana ya tafi jami'ar Jos daga baya ya ketara zuwa jami'a birnin Carlifonia inda ta karanci ilimin shirya fim.
Jarumin ya fara harkar fim gadagadan cikin 1999 kuma yana taka rawa wajen shiryawa da bada umarni har ma rubutun shiri.
Ali Nuhu yana daya daga cikin kusoshin Kannywood da suka raya masana'antar bisa gudunmawar da yake badawa wanda bata da iyyaka.
Dadewar sa tare da nuna basirar shi na wasan kwaikwayo bai tsaya a kan fina-finan hausa kadai, jarumin yana haskawa a cikin fina-finan kudancin kasar ta Nollywood.
Ya samu kyaututuka da dama bisa rawar da yake takawa a bangaren nishadantarwa cikin gida har da kasashen waje.
Jagoran kamfanin FKD yayi sanadiyar fitowar jarumai da dama da ke tashe a masana'antar a halin yanzu.
Yayi murnar cika shekara 15 da auren uwardakin sa jiya laraba 14 ga watan maris. Sakamakon auren nasu Allah ya albarkace su da yara biyuFatima da Ahmad.
Yau take ranar haihuwar shi, muna masa barka da farin ciki na cika shekara 44 a duniya.