Advertisement

An haramta kiran sallah da lasifika a kasar Rwanda

Kungiyar al'ummar musulmin Rwanda ta soki matakin, inda daya daga cikin jagororin kungiyar ya ce wannan ba shi ne matakin da ya kamata gwamnati ta dauka ba.
Advertisement

A labarin da BBC ta fitar gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne saboda yadda kiran sallan ke damun mutanen da ke makwabtaka da masallatan musamman a shiyar Nyarugenge inda masallaci mafi girma a kasar yake.

Advertisement

A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta amince a dinga rage karar lasifika a lokacin kiran Sallan.

Rwanda ta kafa wata sabuwar doka da za ta kula da lamurran gudanar da addini a kasar.

Wannan matakin ya biyo bayan  kulle wasu wuraren bautar yan addinin kirista a fadin kasar mara tsari.

A kwanan baya ma gwamnatin Rwanda ta rufe coci sama da 700 saboda dalilai na tsaro da kiwon lafiya.Sannan an kame malaman coci da dama.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement