Matar shugaban kasa Aisha Buhari ta taya gwamnati da al'ummar yankin gabashin arewa na kasar murna da aka kaddamar da sabon ma'aikatar arewa maso gabas wato North East Development Commission (NEDC)
Aisha Buhari ta taya al'ummar yankin arewa maso gabas murna da samun sabon hukuma
Uwargidan tayi kira ga ma'aikatar hukumar da su tabbatar sun gabatar da tsare-tsaren su domin tallafawa al'ummar yankin
A bisa sakon taya murna da kakakin ta malam Suleiman Haruna ya fitar ranar talata a garin Abuja, hukumar zata kasance cibiyar bada agaji ga wadanda rikicin ta'adanci ya shafa.
Kasancewa ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa an kaddamar da hukumar, Aisha Buhari ta nuna farin cikin ta inda take cewa hakika alheri ne kafa hukumar.
Uwargidan tayi kira ga ma'aikatar hukumar da su tabbatar sun gabatr da tsare-tsaren su domin tallafawa al'ummar yankin.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng