Advertisement

Shugaba Buhari ya isa jihar Benuwe

Shugaban a sauka babban birnin jihar daidai karfe 10:43 na safe
Advertisement

Shugaban ya isa Makurdi babban birnin jihar a daidai karfe 10:43 na safe inda gwamnan jihar Samuel Ortom ya tarbe shi yayin da ya sauka daga jirgi.

Advertisement

Shugaban zai gana da sarakunan gargajiya a fadar sarkin kabilar Tiv Farfesa James Ayatse inda da zasu tattauna kan hanyar dakile rikicin dake faruwa a jihar tsakanin makiyaya da manoma.

Wannan ziyara yana cikin shirin ziyaruruka da shugaban zai kain yankunan da rakici ya shafa.

Bayan rahotani da ya samu daga jami'an tsaro shugaban ya sanar da cewa zai kai ziyara jihohin Taraba, Yobe, Benuwe, Zamfara borno da rivers.

Shugaban zai kai  ziyara jihar Taraba a makon da ya gabata.

Advertisement

Jihar Benuwe tana daya daga cikin jihohi da rikici ya faru. Sakamakon rikicin da ya faru tsakanin makiyaya da manoma an salwantar da dukiyoyi da rayuka da dama

Advertisement
Latest Videos
Advertisement