Advertisement

Ziyarar shugaban kasa zuwa jihar Legas

Wannan shine karo na farko da shugaban kasa mai zaman kujera zai kai ziyarar aiki jihar Legas
Advertisement

Shugaban ya sauka a filin jirgin Murtala Muhammed dake nan jihar inda ya samu tarba daga gwamna Akinwunmi Ambode da sauran jami'an gwamnati  safiyar ranar alhamis 29 ga watan maris.

Advertisement

Jim kadan bayan saukar sa shugaban ya kaddamar da sabuwar tashar mota na zamani da gwamnatin jihar ta gina a nan garin Ikeja babban birnin jihar.

Shugaban zai kuma halarci taron lekca na raya zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan jihar kuma daya daga cikin jagororin jam'iyar APC wato Asiwaju Bola Tinubu wanda za'a gudanar a dakin taro na Eko convention center dake garin Victoria Island nan jihar.

Wannan shine karo na farko da shugaban kasa mai zaman kujera zai kai ziyarar aiki jihar Legas.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement