Pulse logo
Pulse Region

An canza sunan jami’a da titi don karrama marigayi tsohon ministan kasa

Shugaban hukumar watsa labarai na jihar Kano Tanko Yakassai ya sanar da haka yau 6 ga watan Yuli

Gwamnatin jihar kano ta amince da canza sunan jami’ar Northwest university dake Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule kano don karrama tsohon ministan  wanda ya rasu ranar litinin 3 ga watan Yuli.

Bisa ga labari da Daily post ta fitar, shugaban hukumar labarai na jihar Tanko Yakassai ya sanar da haka

A bayanin shi yace an yanke shawarar bayan wata zama ta mussaman da gwamnatin jihar tayi da yan majalisa a daren ranar laraba. “Don karrama marigayi Dan masani Yusuf Maitama Sule bisa ga gudumawar da ya bayar ma jihar kano da ma kasar baki daya”

Ya kara da cewa “gwamnanti ta sauya sunan titin dawaki inda gidan marigayi Dan masani yake zuwa titin Yusuf Maitama Sule shi kuwa titin Yusuf Maitama Sule link road an canza shi zuwa Jafaru Dan Mallam link road.”

“Wannan canji ya faru bayan koke-koken mutane da dama na ganin cewa ya kamata gwamnati ta karrama marigayi Dan masanin Kano bayan rasuwar shi”

“A shirye gwamnatin gwamna Abdullahi Ganduje yake na karrama duk wani dan jihar wanda ya sadaukar da rayuwar sa don ganin cigaban jihar”

Marigayi Dan masanin Kano ya rasu a wata asibiti dake masar bayan ya sha fama da rashin lafiya ranar litinin.

An yi jana’izar shi a kofar fadar sarkin kano ranar talata

Don karrama shi gwamantin jihar Kano ta ba ma’aikata hutu ranar talata 4 ga watan Yuli don jimamin rasuwar tsohon ministan nijeriya

Next Article