An miƙa ma babban ɗan wasan kwaikwayo- Jackie Chan- girma na lambar yabomai suna Oscar. Jackie Chan yana da shekaru sittin da biyu.
Ya karɓi wannan lambar a bikin Gwamnoni wanda ake yî shekara-shekara a cibiyar wasa na Hollywood cikin garin Los Angeles, Kasar Amirka. Wannan taro wanda aka yi a ranar goma-sha-ɗaya na watan Nuwamba 2016, shine taro na takwas.
Bayan yá gabatar da fîm fiyé da ɗari biyu, da kuma harkan fîm na shekara hamsin, masu shirya wannan biki na yabon ʼƴan wasa, sun gani daman miƙà ma Jackie Chan lambar yabo domin ƙwarewan shi. Jackie Chan ƙwararre ne ga harkan wasa na ban dariya, faɗan Judo, da kuma faɗan chinese.
A jawabin sa na karɓan wannan girma wanda aka yi masa, Jackie Chan ya yi farin-ciki domin aukuwar mafarkinsa na karɓan lambar yabo na Oscar. Ya bayyana cewa yana da kishi na karɓin lambar Oscar tun lokacin da yake ɗan yaro, tare da Iyaye. Ya yi bayani haka:
" Bayan shekara hamsin da shiga harkar wasan fim, da kuma fita cikin wasanni fiye da ɗari biyu, na karya kasusuwana da yawa. Amma a wannan rana, lambar Oscar ya zama haki na."
Bugu da ƙari, Jackie Chan ya yi jawabi na godiya kamar haka:
"Ina godiya ga jamaʼa masu kallo, garin Hong Kong, gari na, gari mai albarka, garin da ya wadatár da ni. Ina godiya ga Ƙasar China, Ƙasar mu, ina alfahari da zama ɗan ƙasar China. Godiya ga Hollywood, domin abubuwan da na koya a wajen ku, da kuma yadda kun sa na zama shahararren mutum. Ina godiya domin girma wanda aka bayar na gayyatar da ni zuwa wannan taro."
Bayan wannan jawabi, Jackie Chan ya rubuta a kan shafin na Twitter cewa:
"Ina godiya domin girman da aka bani a wannan rana. Ina farin ciki da murna, kuma na rasa kalmomin na nuna yawan godiya".