Pulse logo
Pulse Region

Mawakiya Di'ja ta samu karuwa, ta haifi diya mace

labarin nata ya zo da mamaki kasancewa bata nuna alamun tana dauke da juna biyu ba a cikin bidiyon wakar ta wanda ta fitar kwanan baya

Ta bayyana farin cikin ta da samun karuwan a shafin ta na kafar sada zumunta ta instagram tare yi ma masoyan ta godiya bisa goyon bayan da suke mata.

Kamar yadda ta sanar ta haifi diyar ranar juma'a 9 ga watan maris.

[No available link text]

"Alhamdulillah, Ubangiji Allah sai godiya. Nine mace mafi farin ciki a raye"  mawakiyar kamfanin Mavin ta rubuta.

Di'ja wanda ta saki jerin wakokin kwanan baya tare da bidiyo wanda bai nuna alamun tana dauke da juna biyu ta kasance daya daga cikin fitattun jarumai dake gudanar da ayyukan su cikin sirri.

Auren ta da mijinta Rotimi wanda aka daura cikin shekarar 2015 ya samu albarkar yara biyu namiji da mace.

Next Article