Vanguard sun kawo rahoto cewa mahaifin Omilade Sarki ne mai farkon aji.
An yanke masa hukunci tare da wasu ʼƴan uwa biyu-Shola Oni da Kayode Oni. An kama su da laifin kisa bayan sun kashe wani Suleiman Afolabi a lokacin da sun yi faɗa.
Wannan faɗa ya faru a Unguwar Oshodi a ranar 25 ga watan Disambar, 2012.
Da táke karanta ma duka mutane uku hukuncin kisa, Shugaban Kotu mai suna Kudirat Jose, ta lura da cewa masu laʼanta sún tabbatar da ƙaran su ba tare da wani shakka.
Sún tabbata cewa waɗanda ake zargi da laifi sún aikatá laifin.
A cikín wani takardan kotu, an rubuta cewa waɗannan mutane uku; Omilade, Kayode, da Shola, sun kashe Afolabi a titin Eyin Ogun a Mafoluku cikin Unguwar Oshodi.
Sún sare shi da adduna.