Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yayi bayanin akan dalilin da yasa bai halarci taron gwamnonin jihohi 36 na kasa da shugaba Muhammadu Buhari
Dalilin da yasa ban tafi taron gwamnoni da aka yi a fadar shugaban kasa
gwamnan yace bai halarci taron kasancewa ta ci karo da naɗin sarauta da za,a yi mai
A ranar juma’a 25 ga watan Agusta ne shugaba Buhari ya gana da gwamnonin har da jiga-jigan jam’iyu na kasar
Shugaban jam’iyar PDP mai rikon kwarya Ahmed Makarfi da jiga-jigan sauran jam’iyar adawa sun halarci taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa
Fayose yace bai samu damar zuwa taron don yaci karo da naɗin sarauta da za’ayi mai
Gwamnan yana cewa ; “ina son in sanar ma wadanda ke yada labari cewa ban je taron shugaban kasa da gwamnoni bisa ga wata dalili mara mana su san cewa ban samu damar zuwa taron don yaci karo da ranar nadin sarauta da aka yi mun.” gwamnan ya rubuta a shafin sa na twitter ranar juma’a.
Ya kara da cewa “ manyan baki sun gabata a jihar Ekiti don halarrar naɗin kuma a daidai lokacin na gan sakon taron shugaban kasa”
A baya gwamnan ya fada cewa shugaban yana fama da ciwon tabin kwakwalwa wanda shugaban yayi watsi da wannan zargin
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng