Gwamnatin jihar Kaduna zata yi wa yara miliyan 3 rigakafi cikin kwana 6
Huƙumar kiwon lafiya na kananan cibiyoyi na jihar Kaduna ta ce a shirye take don yi wa yara miliyan 3 masu shekaru 0 zuwa 5 rigakafi don kawar da cutar shan inna cikin kwana 6 daga ranar 6 ga watan Yuli.
Mataimakin mai ruwa da tsaki na fannin ilimin lafiya Hamza Ikara da jagoran ƙungiyar yan jarida kan kawar da cutar shan inna (JAP) Lawal Dagara suka gabatar da wannan bayani ranar talata 4 ga watan Yuli.
A cikin bayanin za’a gabatar da rigakafin daga ranar 6 zuwa ranar 11 na watan Yuli shekara 2017.
“Za’a gabatar da rigakafin a tituna, gidaje har ma da kasuwanni” inji huƙumar.
Ta kara da yiwa iyaye kira na su taimaka su gabatar da yaran su masu shekaru 0 zuwa 5 don yin rigakafin don kawar da cutar shan inna a jihar.
Bayani ya nuna cewa a shirye huƙumar take wajen kaddamar da yin rigakafin a ko wani lungu da ke fadin jihar cikin lumana.
A karshe huƙumar ta yaba ma sarakunan gargajiya, malamai, yan jarida da sauran al’ummar jihar don gudumawar da suke badawa don kawar da cutar kuma tana fatan zasu cigaba da taimakon hukumar.