Wata mace mai ɗinkin kayan al fahari, ta faɗa ma Kotu na Unguwar Jikwoyi a kusa da Abuja, cêwa mijinta yana da Mata da kuma yara shida a asirce.
"Mijina yana da mata a asirce da kuma yara shida"- Mai Dinkin kaya ta kawo kuka a kotu
Wata mace tana neman a kashe aure bayan ta gano cêwa mijinta yana da aure da kuma yara shida.
Hukumar ʼyan Jaridan Najeriya (NAN) sun kawo rahoto na aikace-aikace da kuma shariʼah. Lydia Dallah ta kawo kuka cewa ba ta sanʼ da auren mijin ba, sai bayan an yi ɗaurin aure tsakanin su. Da take shaida a kotu, wannan mai ɗinki ta yi bayani haka:
“Wannan mutum bai sanar da ni game da aurensa ga wata mace daban, kuma bana da labarin cêwa yana da yara shida da matansa.”
“Bayan ɗaurin auren mu, sai na gano duka gaskiya game da alʼamarinsa. Idan na faɗa masa cewa zan tashi daga gidan sa, sai ya ɗora mana barazana da cêwa zai kashe ni”.
Hukumar ʼƴan Jaridan Najeriya (NAN) sun yi rahoto cêwa an kawo ƙara a kotu bayan mijin Lydia Dallah ya duke ta da ƙarfe na fanka mai horan iska domin ta na neman a kashe wannan aure. Ta ƙara bayani haka:
"Ya halakar da dukiya na masu daraja cikin gida. Makwabci sun tsira da ni bayan na yi ihu da kuka." Bayan ya duke ni, sai na tafi kantin magani domin kula da lafiyan jiki na. Sai aka ba ni shawara in kawo ƙara wajen ʼƴan sanda. ʼƳan sanda sun aika masa da gayyata zuwa offishinsu."
Lydia Dallah, ta yi bayanin cewa ta kai ƙara na wannan matsalar wajen iyali da kuma wajen fasto domin warwarewa, amma babu saʼa. Ta ƙara bayani:
"Iyaye na da Fasto, sun shawarce mu, kuma sun roƙe shi domin ya bari mu kashe wannan aure. Ya ce yana da buƙata na tsare yara biyu waɗanda na haifa masa. Ina son kotu da alƙali, su kashe wannan aure, kuma ina son a bani tsaron yara na".
Mijin Lydia (Yakubu) ya yi musu na zargi wanda aka yi masa. Alƙali Labaran Gusau, ya dage sauraren wannan muhawara zuwa ranar 16 Nuwamba.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng