A labarin da jaridar Daily trust ta fitar, shugaban karamar hukumar Alhaji Mustapha Gado ya bayyana cewa, sojoji dake tsare da kauyen sunyi arangama da barayin wanda yayi sakamakon kashe wasu da dama na daga cikin su.
Anyi musayar wuta tsakanin yan bindiga da sojoji, jami'ai biyu sun rasu
Alhaji Gado ya sanar cewa tuni aka tafi da gawar sojojin garin Gusau babban birnin jihar daga garin Anka
Yace jami'an rundunar sojoji biyu suka rasa rayukan su a sakamakon musayar.
Alhaji Gado ya sanar cewa tuni aka tafi da gawar sojojin garin Gusau babban birnin jihar daga garin Anka.
Sai dai bai bayyanar da adadin yan bindigar da suka rasu sanadiyar hartabon.
Idan ba'a manta ba a makon da ya shude mutane 30 suka rasu sakamakon harin da wasu yan bindiga suka kai daidai kauyen Bawar daji.
Kan wannan lamarin Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya bada umarni na a harbe duk wani mai girke da makamai
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng