An samu fashewar bama-bamai a garin maiduguri a daren ranar talata 18 ga watan yuli
A labarin da kamfanin dilancin labarai (NAN) suka fitar, fashewar sun faru tsakanin karfe 10:45 da 11 na dare a babban birnin jihar Borno.
Rahoto ya nuna cewa bam hudu suka fashe lokaci guda yayin da guda biyu suka kara fashewa bayan minti 15.
Wannan ya faru bayan farmakin da wata yar kunar bakin wake ta kai a masallaci wanda ya kashe mutum 12 a safiyar ranar litinin.
Mun samu labari cewa karfin girgijen bama-bamai da suka fashe ya cire rufin gidajen mutane dake garin
Babu tabbatacciyar labari game da illar da fashewar ya haifa.
Amma dai NAN sun kawo rahoto cewa rundunar sojoji sun harbi wasu da suke zargi da yan boko haram wadanda ke neman kai farmaki a garin wanda sakamaƙon harbin ya haifar da jerin fashewar bama-bamai.