Advertisement

An cafke tsohon gwamnan jihar Jigawa a wata taron kaddamar da wani littafi

Former Jigawa State governor, Saminu Turaki.
Former Jigawa State governor, Saminu Turaki.
Za’a tuhume shi bisa ga zargin laifuffuka da ya shafi al’mundahana
Advertisement

Hukumar yaki da rashawa EFCC sun cafke tsohon gwamnan jihar Jigawa Saminu Turaki

Advertisement

Jaridar vanguard ta ruwaito cewa hukumar sun cafke shi ranar talata 4 ga watan Yuli 2017 a wani taron kaddamar da wani littafi a garin Abuja.

Don tabbatar da haka kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren yace, “ menene abun tabbatarwa game da haka? Da gaske ne mun cafke shi”

Tsohon gwamnan wanda yayi shugabancin jihar Jigawa daga 1999 zuwa 2007, ya shiga hannun hukumar bayan neman ruwa a jallo da take yi tun 2014.

Za’a tuhume shi bisa ga zargin laifuffuka 36 wanda ya shafi al’mundahana a babban kotun tarayya dake Dutse, jihar Jigawa.

Advertisement

An samu labari cewa mai sharia S. Yahuza ya bada umurni na a cafke shi bayan rashin zuwansa gaban kotu don ganin ingancin zargin da ake mai

Advertisement
Latest Videos
Advertisement