Advertisement

Tsohon gwamna ya bada mamaki, zai fito takarar majalisar wakilai

Former Kebbi State Governor, Saidu Dakingari.
Former Kebbi State Governor, Saidu Dakingari.
Idan yayi nasarar lashe zaben, Dakingari zai zamanto tsohon gwamna na farko a tarihin siysasar Nijeriya da zai zama dan majalisar wakilai.
Advertisement

Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Usman Dakingari, zai kafa tarihi bayan da rahotanni suka shaida cewa ya siya fom din tsayawa takarar majalisar wakilai na tarayya.

Advertisement

A labarin da jaridar Dailytrust ta fitar, tsohon gwamnan ya karbi fom din takarar a ofishin uwar jam'iyar APC dake Abuja kwanan baya domin wakiltar al'ummar karamar hukumar Suru da Bagudo na jihar Kebbi a zauren majalisar tarayya.

Mafi yawanci tsofaffin gwamnoni sukan komawa majalisar dattawa bayan wa'adin su na mulkin jiha.

Tsohon gwamnan ya fito takarar majalisar dattawa a zaben baya karkashin PDP amma bai yi nasarar lashe zaben ba.

Kamar yadda jama'a ke hasashe tsohon gwamna wanda ya koma jam'iya mai mulki kwanan baya, ya nemi kujerar dan majalisar dattawa amma ya samu tabbaci cewa jam'iyar APC ta ware wannan takarar ga Sanata Abdullahi Yahaya, wanda ya doke shi a zaben 2015.

Advertisement

Bisa ga wannan lamarin wasu ke ganin cewa ya zabi komawa majalisar wakilai na tarayya.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement