An kama wata buduruwa mai shekara 17 domin laifin fyaɗe
Ƴan sandan Ingila sun kama wata buduruwa mai shekara 17, Lestina Marie Smith, domin laifin fyaɗen da ta yi ma wani namiji mai shekara 19. Ta tsoratar da shi a yayin da ta yi masa barazana da wuƙa a wuyansa. Buduruwan ta faɗa ma saurayin cewa idan bai yi jimaʼi da ita, za ta kashe shi.
Kamar yanda muka samu rahoto, wannan buduruwa ta sha ƙwayoyi a lokacin da ta aikata wannan laifi. An rufe ta a kurkuku wanda yake unguwar Saginaw a Ƙasar Ingila bayan an hana a yi mata beli. Idan aka hukuntar da ita, akwai yiwuwa cewa za ta yi duk rayuwanta a gidan yari daidai da buƙatan dokokin Ƙasar Ingila.
An gurfanar da ita a ranar 17 ga watan Janairu, 2017, kuma an karanta mata laifin Fyaɗe, da kuma laifin jimaʼin dole da batsa. Za a gurfanar da ita a ranar 3 ga watan Fabrairu domin yankin hukunci.