Wani ƙungiya mai kulá da hakkin Dan-adam sun yi rahoto cêwa mutane shida daga iyali guda, sun rasu bayan ʼƴan adawa masu goyon bayan gwamnati sun jefa nakiya a birnin Aleppo.
Kananan Yara huɗu suna cikin waɗanda sun rasu cikin dare, bayan jirage masu saukar angulu sun yi bazuwan ganga mai cike da nakiyoyi.
Nakiyoyin sún faɗi akan mutanen Al-Sakhour a Birnin Aleppo na Gabas. Masu kula da hakkin Ɗan-adam na Ƙasar Syria, sun tabbatar da wannan rahoto.
Masu farín hula waɗanda suka rasu, sun kai yawan hamsin da huɗu cikin saʼoi ashirin da huɗu. Sun rasu a birnin Aleppo na Gabas, bayan sojojin gwamnati sun kai hari.
Gwamnatin Ƙasar Syria sun ƙara ƙarfin harinsu cikin birnin Aleppo na Gabas tun ranar Talata, domin fitar da sojojin adawa da kuma kafa sabuwar zango a yankin Aleppo.
Wasu ʼƴan gwagwarmaya sun faɗi cêwa sojojin Gwamnati Syria suna da goyon baya na Ƙasar Rasha ga ƙarfin jefa hari daga sama. Shuwagabanin Babban Birni na Ƙasar Rasha, waton Moscow, sun ƙaryata wannan labari.
An yi rahato cêwa sojojin Gwamnatin Syria sun kewaye birnin Aleppo na gabas. Mutane fiye da dubu ɗari uku, sun maƙale cikin wannan wuri, suna fámá da rashin abubuwa kamar ruwá, abinci, magani da wutar lantarki..
Án raba Aleppo daidai ɓangare biyu. Ɓangaren Gwamnatin Ƙasar Syria da ɓangaren ʼƴan adawa.
Kafin a fara yaƙi, Aleppo shi ne babban birnin na kasuwanci a Ƙasar Syria.
Yaƙ ya ɓarke a cikin Aleppo a tsakiya na shekara 2012.