Pulse logo
Pulse Region

Dalilin da yasa shugaba Buhari ya soke zaman majalisa na wannan makon

Sanarwar tace an dakatar da zaman ne bisa ga ayyukan siyasa da ake fama da shi a kasar a halin yanzu musamman zaben fidda da gwani na jam'iyun kasar.
Nigeria's President Muhammadu Buhari
Nigeria's President Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da zaman majalisar sa da aka saba yi na mako-mako.

A cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Femi Adeshina, ya fitar zaman majalisar gwamnatin tarayya ba zata gudana wannan makon bisa ga wasu dalilai na siyasa.

Kamar yadda sanarwar tace mafi yawancin yan majalisar suna cikin masu gudanar da wadannan zabunan a jihohin daban-daban don haka aka dakatar da zaman wannan makon domin basu damar mayar da hankali wajen zaben.

Zaman majalisar gwamnatin tarayya tana gudana ne a ko wani ranar Laraba cikin mako kuma shugaba yake jagorantar zaman tare da mataimakin sa da sauran ministocin kasar.

Recommended For You

Subscribe to receive daily news updates.