Pulse logo
Pulse Region

JAMB ta dakatar da ma'aikaciyar ta kan Miliyan N36 da maciji ya hadiye a ofishin ta

JAMB ta dakatar da mai laifin Philomina Chieshe wanda ita ce jogaran fanin siya da saiyarwa a hukumar.

A cewar ta mai aikin gidan ta tare da abokiyar aikin ta Joan Asem suka hada hannun wajen wawushe kudin ta hanyar tsubbu daga asusun ajiya na hukumar.

Dangane da zargin, kakakin hukumar JAMB Fabian Benjamin ya sanar cewa an gayyaci jami'an tsaro domin yin bincike a kan batun.

Yana mai cewa "An dakatar da ita kuma a yanzu tana fuskantar hukuncin ladabtarwa kafin a gama bincike kan lamarin. Tayi ikirari cewa maciji ya hadiya miliyan N36 na hukumar."

Shi dai wannan lamarin ya haifar da cece-kuce tsakanin yan kasar inda dubban mutane a kafafen sada zumunta suna ta kushe wannan ikirarin da tayi na cewa maciji ya hadiye hadiye kudi har miliyan N36.

Subscribe to receive daily news updates.

Next Article