Advertisement

Sojoji sun kashe wani dan fashi, an gano bidigar AK 47 guda 2

Kakakin rundunar sojoji na kasa Brig.gen Sani Usman ya sanar da haka a wata takarda da aka fitar ranar juma’a
Advertisement

Rundunar sojoji na 1 Division sun kashe wani daga cikin yan fashi da makami a karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara ranar alhamis.

Advertisement

Kakakin sojoji na kasa Brig.gen Sani Usman ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar juma’a.

Usman yace sojojin sun kawar harin da yan fashi ke neman yi ga al’ummar yankin.

Yace yan fashi sun kashe wani jam’in hukumar FRSC kafin zuwan sojoji.

Usman yace sojojin sun gano bindigar AK-47 guda biyu da kunshin harsashin bindiga 6 da kuma babura 7 daga yan fashin.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement