Advertisement

Kuka da hawaye a wajen binnen Kanar Abu-Ali da sojoji shida waddanda sun rasu.

___5724057___https:______static.pulse.com.gh___webservice___escenic___binary___5724057___2016___11___8___6___unnamed
___5724057___https:______static.pulse.com.gh___webservice___escenic___binary___5724057___2016___11___8___6___unnamed
Abba Kyari-Shugaban Maʼaikata na Offishin Shugaban Kasa ya wakilta da Muhammadu Buhari a janaʼizar sojojin da suka rasu.
Advertisement

Shugaban sojojin Najeriya da masu nuna juyayi sun yi kuka da hawaye a lokacin da aka binne Babban mai yaƙi-Kanar Muhammad Ali yau a garin Abuja.

Advertisement

ʼYan Boko Haram sun kai harin dare a garin Mallam Fatori cikin Jihar Borno. Sun kashe Abu-Ali da da wasu sojoji. Sunayen waddanda suka kashe: Muʼazu Ibrahim, Hassan Jafaru, Bassey Okon, Chukwu Simon, da Patrick Paul.

Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya yi ƙaramin jawabi a Makabartar Kasa a lokacin da yake yaba ma waddanan sojojin da suka faɗi. Ya yabi ƙarfin ziciya, koƙari da kuma mazakuta na marigaya.

Wannan hari ya faru a lokacin da Abu-Ali ya gudanar da aiki na ʼyantar da garin Baga wanda yake hannun Yan Boko Haram da kuma sauran yaƙi wanda ya aikatar ma yan taʼada.

Wannan rasuwa ya kawo baƙin-ciki da makoki ga mutanen ƙasar Najeriya gaba ɗaya.

Advertisement

Muna fatar Allah ya gafartar musu. Allah ya yi musu rahama. Allah ya albarkace su da Al-jannah Firdaus.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement