ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin jihar Kano tayi maraba da wa'adin shugaban kasa

Sanarwar tace an samu karin masu tsaka jari a kasa bisa shirin tabbatar da adalci gwamnatin yanzu ta kafa

Labarin haka yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishnan labarai da al'adu Mallam Muhammad Garba ya tura wa manema labarai a garin Abuja.

Sanarwa ta nuna cewa zarcewan shugaba zai taimaka wajen daura daga inda ta tsaya na shirin wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da harkar tsaro tare da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da adalci a ko wani fanni na gwamnati wanda ta fara shekara uku da hawa mulki.

Sanarwar tace an samu karin masu tsaka jari a kasa bisa shirin tabbatar da adalci gwamnatin yanzu ta kafa.

Hakalizalika matakin kawar da cin hanci da rashawa da yaki da ta'adanci ba tare da jinkiri da gwamnati keyi ya taimaka wajen gina martabar kasa a idon sauran kasashen duniya.

ADVERTISEMENT

A ranar litinin ne  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da wa'adin tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa.

Lamarin ya tada kura a kasa inda har zuwa yanzu ana ta cece-kuce kan batun a kafafen sada zumunta.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT