ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kwana 5 bayan zama zakarun turai, jagoran Real Madrid ya ajiye aiki

Zidane ya ajiya aikin sa bayan ya jagorancin kungiyar wajen cin kofin nahiyar turai karo na 13 kuma na uku a jere.

Dan kasar Faransa yayi yanke shawarar ne inda ya gayyaci yan jaridu domin fitar da matakin da ya dauka.

Kamar yadda majiya suka ruwaito, mai horas da yan wasan ya dauki matakin ajiye aiki bisa facin baki da yan wasa Cristiano Ronaldo da Garreth Bale suka yi na cewa wata kila zasu bar kungiyar.

Yayin da ya zanta da manema labarai kan matakin da ya dauka, Zidane ya bayyana cewa zai bar kungiyar ne domin neman canji kana yayi dinbim masoyan kungiyar godiya bisa damar da aka bashi na jagorantar ta.

Sai dai bai bayyana inda zashi daga nan ba.

ADVERTISEMENT

Tsohon dan wasan kungiyar ya maye gurbin tsohon jogaran ta, Rafa Benitez a cikin 2016 wanda daga bisani yayi nasara lashe wasu muhimman kofi.

A tsawon shekara biyu da watanni da yayi a kungiyar yayi nasara lashe kofin UEFA champions League sau uku da La liga da kofin UEFA super sau biyu da kuma kofin gasar FIFA club world cup sau uku.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT