Advertisement

Buhari zai kai ziyara kasar Ingila

shugaban zai gana da firayi ministan ingila Theresa May kafin ya halarci taron shugabannin kasashe rainon-ingila wato commonwealth
Advertisement

Wannan labarin ya fito a wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu, ya fitar ma manema labarai.

Advertisement

Sanarwar tace shugaban zai gana da firayi ministan ingila Theresa May kafin ya halarci taron shugabannin kasashe rainon-ingila wato commonwealth.

Shugaban zai kuma tattauna da shugaban kamfanin Dutch royal plc mista Ben van Beurden da kamfanin Shell da makamantan su kan matakin zuba jari a masana'antar mai na kasar Nijeriya.

Kakakin ya kuma sanar cewa shugaban zai tattauna da Archbishop na Centebury Justin Welby, wanda yake abokin shine domin inganta zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Daga karshe shugaban zai gana da wasu jami'ai na Ingila da kuma yan Nijeriya mazaunan kasar.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement