Advertisement

Sanadiyar satar rago wani bawan Allah zai dukufa a kurkuku

Shi dai ragon da aka sata mallakar Kehinde Yekinni ne kuma an kiyasta adadin kudinta kan naira dubu saba'in da biyar (N75,000)
Advertisement

Babban majistare Mista S. O. Benwo ya yanke hukuncin bayan wanda ake zargi ya bada amsar aikata hakan.

Advertisement

Wanda aka yanke  ma hukunci yana zaune ne a layin Bamidele mai namba 14  a Ota ya amince da aikata laifin satar, da cewar halin yunwa ce ta sa ya saci ragon.

Shi dai ragon da aka sata mallakar Kehinde Yekinni ne kuma an kiyasta adadin kudinta kan naira dubu saba'in da biyar (N75,000).

Mai gabatar da kara Sajen Chudu Gbesi ya shedawa kotu cewar wanda aka yankewa hukuncin yayi satar ne ranar 13 ga watan Janairu, wajen karfe biyar da rabi na dare, a wurin tsayawar mota na Bible collage dake cikin garin Ota.

Mai gabatar karar ya ce,laifin da aka aikata ya sabawa sashe na 390 (9) karamin sashe na tara na dokokin   masu laifi na Ogun shekara ta 2006.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement