Advertisement

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana anniyar sa na zaben 2019 (Ga bidiyo nan kasa)

Jigon jam'iyar APC ya sanar cewa ya shirya tsiratar da kasa ta hanyar samun cigaba
Advertisement

A cikin wani bididyo dake zagayawa a duniyar gizo tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyanar anniyar sa na tsayawa takara a zaben 2019.

Advertisement

A busa rahoton jaridar vanguard an samu bididyon daga wani bawan Allah wanda ya nemi a asirtar da sunan shi.

Atiku ya bayyana haka ga jama'a bayan mutane da dama na ta jiran sammani ko zai bayyana anniyar sa tun da wuri ko sai dab da lokacin zabe.

A cikin bididyon jigon jam'iyar APC ya sanar cewa ya shirya tsiratar da kasa ta hanyar samun cigaba.

A baya dai gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-makura ya bayyana cewa babu wanda yafi cancanta a jam'iyar APC illa Shugaba Muhammadu Buhari.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement