Advertisement

Buhari zai halarci taron majalisar dinkin duniya a Amurka

kakakin shugaban kasa shehu sani ya tabbatar da haka
Advertisement

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi a babban taro na majalisa dinkin duniya da za’a gabatar a kasar Amurka.

Advertisement

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da haka kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.

Shehu ya tabbatar cewa shugaban zai yi jawabi a taron majalisar dinkin duniya da za’a gabatar da kasar Amurka.

“Babu tabbatacciyar ranar da zai bar kasa don yana iya canzawa amma dai na san ana sa ran cewa zai yi jawabi a taron. Don haka na san zai halarci taron kuma zai yi jawabi.” inji kakakin.

Buhari shine Shugaba na bakwai da zai yi jawabi a taron majalisar da za’a gabatar.

Advertisement

Zai yi jawabi bayan shuwagabannin kasar Brazil, Amurka, Guinea, Switzeland, Jordan da Slovakia.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement