Advertisement

An saki direkta wanda aka yi garkuwa dashi

Rundunar yan sanda na jihar ta tabbatar cewa direkta wanda aka saki a safiyar ranar lahadi ya koma ga iyalin shi
Advertisement

Rundunar yan sanda na jihar Kaduna ta tabbatar cewa a ranar lahadi aka direkta wanda ke aiki a ma’aikatan karatu na jihar ya samu yanci daga wadanda suka yi garkuwa dashi.

Advertisement

Kakakin yan sanda  ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da haka ranar lahadi yayin da ya gana da manema labarai na NAN.

Ya bayyana cewa direktan wanda aka saki safiyar ranar lahadi ya koma ga iyalin shi.

Aliyu ya sanar cewa wata mata mai shayarwa wanda aka saci tare da direktan ta samu yanci itama.

Kakakin bai sanar ko akwai fansa da aka biya don su samu yanci daga wadanda suka sace su.

Advertisement

Aliyu yayi kira ga yan jihar da su cigaba da taimakon jami’an tsaro wajen bada labari  da zai taimaka masu wajen magance ire-iren miyagun ayyuka da aukuwa a jihar da ma kasar baki daya.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa an saci John Gorah a tsakar daren ranar 3 na watan Satumba a gidansa dake Mararaban rido na jihar Kaduna.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement