Wata ƙungiyar agaji mai suna ‘victim support fund’ (VSF) sun tallafa ma yan gudun hijira 2000 wadanda riƙicin yan ta’ada (boko haram) ya shafa da miliyan N40 don tafiyar da sana’ar noma, ranar al’hamis a garin Jalingo.
Yan gudun hijira masu noma 2000 sun samu naira miliyan N40
Sakataren asusun taimaƙo yace asusun zata cigaba da tallafa ma yan gudun hijira don su ma suyi zaman kansu
Sakataren kungiyar farfesa Sunday Ochoche yace wannan yana daga cikin tsarin ƙungiyar don suma yan gudun hijira su kasance suna dogara da kansu a duk inda suka sami kansu.
Yace asusun kungiyar zata cigaba da tallafa wa yan gudun hijira.
Inda yake bada nashi ra’ayi, sakataren gwamnatin jihar Taraba mista Anthony Jellason ya yaba wa ƙungiyar bisa ga tallafawa da suke yi ma yan gudun hijira da riƙicin yan ta’ada ya shafa.
Yayi kira ga ƙungiyar VSF da su kara tsarin taimaƙon da suke don riƙicin da ya faru a garin Takum, Ussa da Gembu kwanan nan.
Ya tabbatar cewa gwamnatin gwamna Darius Ishaku tare da haɗin gwiwan gwamnatin tarayya zata nemi hanyar tabbatar da tsaro a kasar.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng