Mai tsare bayan Manchester united Eric Baily ba zai samu damar buga wasan da united zata yi da Real madrid a ranar 8 ga watan Agusta bisa ga dakatar dashi da hukumar UEFA tayi
Mai tsare bayan manchester united ba zai buga wasan da ƙungiyar zata yi da Real madrid
Eric Baily ba zai buga karawan da United zata yi da Real kasancewa UEFA ta tsawaita akan hukuncin dakatar da shi na wasa uku
Baily ya samu jan kati a karawa da united tayi da celta vigo cikin watan mayu a gasar europa cup.
Sanadiyar haka UEFA ta dakatar dashi har wasa uku kuma dan wasan ba zai samu damar buga karawa da united zata yi da real.
Hakazalika dan wasan ba zai buga wasan farko da united zata yi a gasar zakaran turai watau UEFA champions league.
Dan ƙwallon mai shekaru 23 ya dawo united a shekara 2016 daga Villareal.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng